RAYUWA A AREWA NAN DA 2040...
Wasu daga munanan al'amurra da ke
addabar Arewa da babu wata taswira ta yimusu gyara na dindindin sune
1 Hauhawan jahilci tsakanin matasa
Shekaru 20 baya ba gagara tallafin ilmin
zamani yayi wa Arewa ba, bata kammala
amincewa da Shi bane. Sai dai a yanzu da ta
kammala amincewar an sami hauhawar
haihuwan Yaran da iyayensu ba zasu iya
basu ingantaccen ilmi ba. A yayinda talakan
da ke da karfin bayar da ilmi ga yara 3 ya
haifi yara 10, akwai yiwuwar daya ne tal zai
iya samin ilmin yayinda ragowar tallafin
ilmin na mutum biyun zai dulmiye a kudin
cefanen abinci kenan a tsakanin iyaye
talakawa goma zasu iya samar da jahilan
matasa akalla guda 90 Wanda zasu zamo
nauyi ga shekara 21 masu zuwa- Akwai
sakamakon bincike akan hakan-
2 KYAMAR JAHILCI
A yayinda duniya ta dunkule ta koma cikin
wayar hannu da ba a iya sarrafawa sai da
ilimin rubutu da karatu na wasu manyan
yarukan duniya har ta kai a manyan Birane
daga cefane, tasi, har me kwasan shara
akwai manhajar da aka tanada a waya don
kiransa ya zo har kofar gida don biya maka
bukata. Nan da shekara 20 zai yi wuya a
sami wani gurbi da zai saura don yin hulda
da jahili. Wannan na nufin akasarin yan
cirani dake yin hijira zuwa alkarya don yin
wasu aiyuka da aka sauwake wa jahilci su
ma zasu fara rasa hurabensu. Misali a garin
Abuja samfurin motocin Uber da texify sun
tilastawa daruruwan direbobi yan cirani rasa
aiyukansu sakamakon kasa iya sarrafa
manhajar Uber din akan wayoyinsu saboda
rashin karatu ko yaya duk kuwa direbobin
yan cirani sukan fi saukin kudi da sanin
hanya, Amma basu da saukin samu akan
wayar hannu ta zamani.
3 Rashin aikin yi.
Rashin aikin yi na iya nunkuwa a Arewa
duba da yadda gwamnatin Arewa ta kasa
samar da guraben aiyuka ga matasa ko
basu dalilan iya kirkirar aiyuka ta hanyar
wadata yankin da wutan lantarki, da ruwan
sha da ilmi mai rahusa, maimakon yin hakan
Gwamnatocin sun fi mai da hankali ga gina
ababen da zasu baiwa dan Arewa damar
sake zabensu maimakon gina dan Arewa,
misali gina gadoji da manyan tituna da
bayar da kudin cefane na babu gaira babu
dalili a matsayin jarin da ba a tanadi wajen
juya shi ba. Ko kuma baiwa mata tulunyar
suyan kosai da ba zata gaza yin tsatsa ba
nan da shekaru2 masu zuwa. Tare da tilasta
Dan Arewa yayi noma ba tare da wani
ingantaccen shirin noma ba
Wannan lamari ba za a gane illarsa sai
gwamnati ta bar Arewa zuwa kudu nan da
shekara 4 in Da akwai yiwuwar bazata dawo
ba sai bayan wasu shekaru 16 wato dai nan
da shekara 20 bayan ciwon ya rika.
4 MATSALOLIN AL'UMMA
Kasawar malamai da masu fada aji wajen
dakile matsalar mace-macen aure dake yin
illa ga tarbiyar yara fiye da illar da yake yiwa
maauratan, da matsalar Almajirci da yakinta
ke samin tarnaki ko dai daga kungiyoyi
masu ci da gumin almajirai, ko gidajen
malaman da ke daurewa almajircin gindi
saboda suna da maslaharsu a ciki ko no
kuma daidaikun mutane da ke amfana da
almajiran wajen aiyukan gidansu cikin sauki
ko ma uwa uba iyayen da ke yin cikin
almajiran su haifa su turo su bara ba tare da
an sami hanyar dakatar dasu ba. Wannan da
ma wasu dalilai da suka hada da mace
macen iyaye a dalilin rashin tsaro ko rashin
ingantaccen kiwon lafiya zasu sake ninka
Yaran da basu sami tarbiyar iyaye ba a
Arewa a dalilin ko dai mutuwar aure ko
mutuwar iyaye ko hijirar yara daga gaban
iyaye wanda nan da shekaru 20 ragamar
raino zata iya shiga hannun wadanda basu
sami raino ba Da kaso 45 cikin dari ( Bincike
ne)
5 MATSALAR MUHALLI
Sama da shekaru 30 kenan akasarin yan
Najeriya musamman ma yan Arewa suka
hakura da samin kashi 70 daga moriyar
Gwamnati ta hanyar ruwa da wutan lantarki
inda neman ruwa da fetur ya shiga lissafin
ababen da suka hana dan Najeriya kishin
gwamnatocinsa ko ganin mutuncinsu
saboda kasa share masa hawaye da suke a
wannan fannin da ya fi kowane fannin
kyautata rayuwa zama wajibin Gwamnati.
Hakan ta sanya idaniyar ruwa ta fara zaizaye
karkashin yankuna mafi tsoka a Arewa
sakamakon yin Borehole barkatai har ta kai
zaka iya samin gidaje 5 a jere kowanne da
Birtsatsai wanda daya kacal zai iya basu
ruwa dukansu. Ga masallatai da nasu, ga na
'yan siyasa masu neman kuri'a duk bayan
shekaru 4 zasu so su yi. Gefe guda wani
bincike ya tabbatar cewa mutanen layi me
dauke Da gidaje 20 Na shakar konanannen
fetur da injin oil na akalla lita70 tsakanin
kowacce karfe7 zuwa 11 na dare. Abinda me
iya janyo karuwar masu cutar da ta shafi
kayan ciki su ninka zuwa kashi 50 nan da
shekaru 20.
A cikin wannan babin bamu tabo illar da
ta'ammuli da rashin tsafta da ingantaccen
kiwon lafiya da rikon sakainar kashi ga kaida
ke shirin yi ba. Sai a rubutu na gaba
inshaAllah inda zamu kutsa kan shaye-
shaye. Copy from Rahma Abdulmajid

1 Comments
Allaah yasa mudace
ReplyDelete