Header Ads Widget

Responsive Advertisement

KARAYAR ARZIKI A KASAR HAUSA.....!!!

A baya ina karami nasan sama da mutane 20 a lokon anguwannin mu da suke fidda Zakkah duk shekara.

Allah kuwa ya albarkaci dukiyarsu har suka bar duniya suna cikin rufin asiri da kuma kyakkawar Zuriyar da suka bari.

Amma a yau nasan Samari sama da 100 da suka mallaki jari na kasuwanci sama da miliyan 5,amma ban taba ji ko gani ba.

Mutane da dama daga 'yan kasuwa da 'yan boko da Malaman boge duk basa bada Zakkah don kawai tsabar yiwa Allah rowa.

Wan nan ne yasa sai kayi ta ganin masu karayar arziki a cikin mu kamar zubar ruwan damina.

Allah yana tsarkake dukiyar musulmi daga masifu idan yana fitar da hakkinTalakawa da ya dora musu.

Amma shi kafiri bashi da halal ko haram kamar dabba yake.

  • Allah ya bamu Arziki ya kuma bamu ikon fidda hakin dukiyar daya bamu.

Post a Comment

0 Comments