Header Ads Widget

Responsive Advertisement

IDENTITY THEFT

IDENTITY THEFT SATAR SIFFA Daga cikin miyagun Miyagun Hanyoyin abotar kafar sadarwar wan nan zamanin Akwai “Identity theft” wato satar Siffa, Nasan da yawa wasu zasuce minene satar Siffa ? Ko Kuma taya ake satar siffar mutum a kafar sadarwa ? Kamar yanda satar mutane yazama ruwan dare a wan nan zamanin haka satar Siffa Shima yayi katutu cikin Al'ammur mu. Banbanci shine A masu satar mutane sunayi ne gaba ɗaya a daina ganin mutum ko Jin ɗuriyarshi Wanda su Kuma Masu satar Siffa zasu sace mutum wani lokacin baima sani ba sai idan ansanar dashi. Wani lokacin Kuma sukan saci Siffar mutum idan Asiri yatuno yagane saisu nemi yabasu kuɗin fansa kamar yanda masu garkuwa da mutane keyi. Wata ƙila masu karatu suyi mamaki taya za'ace Ansace mutum bai sani ba ? Wan nan yana faruwa ne a lokacin da wani yayi nasarar sace kalmomi ko bayanan sirrin dakake Amfani dasu wajen shiga Shafinka harta kai ga ya haukan shafin yaci gaba da gudanar da mu'amala batare da sani ko yardarka ba. Wan nan Satar itama Ana Amfani da miyagun hanyoyi ne irensu “Guessing Ko Brute Forcing” da dai sauransu. Wan nan dambarwar tafi faruwa ga masu saka lambobin tsaro Acikin Lambar wayarsu Kuma ya kasance basuyi ɓoye Lambar wayarsu ba. Misali inada Lambar waya 07063982091 sai kawai idan nazo saka Password sai nasaka “982091” kaga dazarar Anyi Guessing za'asamu damar ɓalla Shafin. Hanya ta uku za'aiya sace Siffar ka batare da kasani ba Saboda ba'achanza Password ba Ballantana kazo shiga kagane haka zalika ba'ayi dogon motsin da zaka gane ba galibin masu Amfani da wan nan hanyar sunayi ne don, Sauraro ko ganin irin wainar da kake toyawa mafi yawan masu Amfani da wan nan hanyar Ana kiransu ƴan leƙen Asiri galibin irin wan nan yafi faruwa a kafar sadarwa “Twitter, Ko Email” Hanya ta huɗu Ana'iya sace Siffar Mai shafi A Dandalin abota ta hanyar kwafar irin bayananshi da hotunshi da Lambar wayarshi, wan nan itace hanya mafi muni Wacce tafi faruwa ga Manyan mutane ko Kuma wasu sanannu (Celebraty). Da wan nan hanyar Ana iya yaudarar mutane da dama Misali Akwanaki baya Ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Nigeria wato AHMAD MUSA” Yafito yana bayani A wani Fai-fan bidiyo daya ɗora A Shafinsa inda yake Kira da A ƙauracewa mu'amala ta kuɗi da wani Shafi da'aka buɗa Mai ɗauke da Sunan AHMAD M MON"

Post a Comment

0 Comments